'Yan sandan Nijeriya sun tabbatar da kone gidaje 11 kurmus a jihar Taraba tare da kashe mutum daya, yayin da mazauna gari suka ce mutum bakwai aka kashe, a wani rikici tsakanin kabilun Mumuye da Fulani na da ya hada da yankunan Lushi, Sukuwa, Hore Ladde da kuma Garin Dogo na karamar hukumar Lau dake jihar Taraba.
Daruruwan mutane ne suka bar gidajen su saboda neman mafaka a makwabtan kauyuka saboda rikicin wanda ya fara da safiyar Juma'ar da ta gabata.
Masu gudu daga garuruwan suka ce rikicin ya samu asali ne daga rashin jituwa akan wani kogi da kauyukan biyu suka yi. "Wasu matasan Mumuye daga kauyen mu sun kawo mana harin mikiya," inji Florence Danladi, 'yar garin da rikicin ya shafa.
"Wannan harin ban mamakin da wasu kashe-kashe shine babban abunda ya janyo rikicin nan da yake faruwa yanzu."
Wani basaraken gargajiya wanda ya nemi a sakaye sunan shi yace "abin ya fara ne akan wata kogi, daga baya sai aka fara musayar duka tare da kone wasu gidaje.
"Sannan kawo yanzu, kusan dukan garin Lushi da Garin Dogo an kone su."
Amma da aka tuntubi kakakin 'yan sandan jihar Taraba yace mutum daya ne kawai aka kashe indq aka kone gidahe sha daya.
Yace 'yan sandan kwantar da tarzoma na yankin saboda shawo kan lamarin.
Wannan rikicin yana zuwa ne bayan makwanni kadan da aka samu wani rikicin tsakanin yankin Shongom da Jole, na karamar hukumar Lau, da suka samu rashin jituwa akan wani lambun kiwon kifi inda aja kashe mutane da dama.
Title :
An Kashe Mutum 7, An Kone Gidaje Shida A Rikicin Taraba
Description : 'Yan sandan Nijeriya sun tabbatar da kone gidaje 11 kurmus a jihar Taraba tare da kashe mutum daya, yayin da mazauna gari suka ce mutum...
Rating :
5