Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Saki El Zakzaky Ba - Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban kasa ta jaddada cewa ba za a saki Shugaban Kungiyar Shi'a ta kasa, Malam Ibrahim El Zakzaky ba saboda batun sakinsa ya jibinci sha'anin tsaron kasa da kuma ra'ayoyin jama'ar kasa.
Fadar Shugaban kasa ta yi nuni da cewa sha'anin El Zakzaky ya wuce batun kotu kuma dokar kasa ta fifita tsaro da kuma ra'ayin jama'ar kasa a kan bukatar wani mutum guda.
A cewar Fadar Shugaban kasa, Uwargidan El Zakzaky wadda ke tare da shi a inda ake tsare da shi, za ta iya yin tafiyarta saboda jami'an tsaro sun tsare ta ne saboda duba lafiyarta don ta samu rauni a lokacin da aka kai samame gidan mijin nata.
Title :
An Ba Wa Matar El Zakzaky Daman Tafiya
Description : Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Saki El Zakzaky Ba - Fadar Shugaban Kasa Fadar Shugaban kasa ta jaddada cewa ba za a saki Shugaban Kungiyar Shi...
Rating :
5