Tsohon Gawmnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce matukar Allah ya kaddara zai zama shugaban kasar Nijeriya, to babu wani mutum da ya isa ya hana komai karfinsa.
Lamido wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya nuna bacin ransa kan yadda gungun 'yan sanda suka hana magoya bayansa yin taron nuna goyon bayansa a garinsa na Bamaina.
Tsohon Gwamnan ya ce shi bai taba ganin inda aka ce wai sai ka nemi izini kafin ka yi taro kai da masoyanka ba.
"Ubangijin da ya baiwa Tafawa-Balewa, Ironsi, Gowon, Murtala, Shagari, Buhari, Babangida da Jonathan mulki, shi zai ba ni idan ya ga dama. Don haka babu wani tasiri da karfi ko iko zai yi", inji Lamido.
Daga Rariya
Title :
Allah ne Kadai Zai Hana Ni Zama Shugaban Kasa A 2019, - Sule Lamido
Description : Tsohon Gawmnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce matukar Allah ya kaddara zai zama shugaban kasar Nijeriya, to babu wani mutum da ya i...
Rating :
5