Sabbin Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya arce zuwa yankin Kala-Balge da ke iyaka da kasar Kamaru ta gefen dazuzzukan da ke gabar tekun Chadi bayan an fatattake su daga Dajin Sambisa.Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an ga Shekau a kauyen Pulka da ke kusa da garin Gwoza a kan hanyarsa na zuwa yankin Kala-Balge kuma ana ganin yana tare da wasu daga cikin 'yan Matan Chibok wadanda yake amfani da su a matsayin garkuwa.
Shugaban Kungiyar Masu kamun kifi a tekun Chadi na jihar Borno, Abubakar Gamandi ya nuna cewa Shugaban Bangare na Boko Haram, Abu Musab Al-Barnawi ya rigaya ya isa yankin na Kala- Balge tun a watan Agusta bayan ya balle daga uwar kungiyar.
Daga Naij Hausa
Masana yankin sun nuna cewa yankin na Kala- Balge yana da ciyayi masu tsawo saboda kusancinsa da Kogin ta yadda zai yi wahala ga jiragen sama su iya gano inda suke boye ba ya ga yawan kifi da za su rika samu don ci gaba da rayuwa.
Title :
Abubakar Shekau Ya Arce Zuwa Kala-Balge
Description : Sabbin Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya arce zuwa yankin Kala-Balge da ke iyaka da kasar Kamaru ta gefen dazu...
Rating :
5