Kungiyar 'yan uwa Musulmai ko kuma Islamic Movement of Nigeria bai bin tafarkin Shi'a, ta ce, ta yi farin ciki da hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke na a saki shugabanta, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
A ranar Juma'a ne dai alkalin wata babbar kotun Najeriya, Mai shari'a Gabriel Kolawole, ya yanke cewa gwamnati ta saki Elzakzaky cikin kwana 45.
Sannan kuma a ba shi diyya shi da mai dakinsa ta Naira Miliyan 25 kowanennen su.
Kotun ta kuma umarci gwamnati da ta gina wa shugaban na IMN gida a duk inda yake so kasancewar an ruguje gidansa.
To sai dai wasu jiga-jigan 'ya'yan kungiyar sun fara yin tsokaci dangane da batun sake gina gidan a Zaria ko kuma a wani gari daban.
Malam Abdulhameed Bello wanda shi ne jagoran 'yanuwa musulmin a Zaria, ya ce, sun yi murna da jin hakan amma fa ba ya tunanin El-zakzaky zai so zama a wani gari sabanin mahaifarsa, Zaria.
Tun dai watan Disamba Elzakzaky yake tsare a hannun gwamnatin Najeriya, bayan wani farmaki da sojojin kasar suka kai wa mabiyansa bisa zargin yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar.
Title :
Zai Wuya El-Zakzaky Ya Bar Zaria'
Description : Kungiyar 'yan uwa Musulmai ko kuma Islamic Movement of Nigeria bai bin tafarkin Shi'a, ta ce, ta yi farin ciki da hukuncin da babbar...
Rating :
5