Hukumar Da'ar Ma'aikata ta Kasa ( CCB) ta fito fili ta bayyana cewa za ta tuhumi akalla ministocin gwamnatin Buhari su 18 bisa kin mutunta hukumar wajen fayyace adadin kadarorin da suka mallaka kamar yadda doka ta tanada.
Shugaban Hukumar ta CCB, Sam Saba ya ce ministocin sun ki amsa gayyatar da hukumar ta gabatar masu don su fayyace adadin kadarorin da suka mallaka inda kuma ya yabawa Shugaban Rundunar Sojan kasa, Janar Tukur Burutai da takwaransa na 'Yan sanda, Sufeto Janar Ibrahim Idris wadanda suka bayyana Kadarorinsu a kan lokaci.
Ministocin da ake tuhuma bisa bayanin da ya fito daga hukumar CCB sun hada da Ministar Kudi, Kemi Adeosun, Ministan Ma'adinai, Kayode Fayemi, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu Ministan Wutar Lantarki da Ayyuka, Babatunde Fashola, Karamin Ministan Mai, Ibe Kachikwu, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu.
Sauran su ne, Shugaban Hukumar Kula da Rundunar 'Yan sanda ta kasa, Mike Okiro, Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, Karamini Ministan Ma'adinai, Abubakar Bawa Bwari sai Ministan Suduri, Rotimi Amaechi,
Sai Ministan Harkokin Mata, Aisha Alhassan, Ministan Wasanni, Solomon Dalung, Ministan Kasafin Kudi, Udo Udoma, Ministan Tsaro, Dan Ali Mansur, Karamin Ministan Muhalli, Ibrahim Usman Jibril, Ministan Albarkatun Ruwa; Suleiman Adamu, Ministan Yada Labarai, Lai Muhammed, Karamin Ministan Hasken Wutar Lantarki, Mustapha Baba Shehuri , Ministan Harkokin Yankin Neja Delta, Claudius Daramola.
Daga Rariya
Title :
Za A Tuhumi Ministoci 18 Bisa Kin Bayyana Kadarorinsu
Description : Hukumar Da'ar Ma'aikata ta Kasa ( CCB) ta fito fili ta bayyana cewa za ta tuhumi akalla ministocin gwamnatin Buhari su 18 bisa kin ...
Rating :
5