Hukumar kula da kotuna ta kasa ( NJC) ta bayar da shawarar sallamar Alkalin Babban kotun jihar Abia, Mai Shari'a Ugbo Ononogho da kuma yi wa Alkalin kotun jihar Zamfara, Mai Shari'a Umar Nasir Gumi ritaya bisa zargin laifin cin hanci da rashawa.
Tuni dai hukumar ta dakatar da Alkalan biyu har sai bayan gwamnatocin jihohinsu sun amince da shawarwarin da hukumar ta gabatar kan Alkalan. Tun bayan da aka cafke wasu Alkalai guda bakwai ne, hukumar da ke kula da kotunan ta mayar da hankali wajen duba koke koken da ake gabatar mata kan wasu Alkalai na kotunan tarayya da na jihohi.
Title :
Za A Sallami Wasu Alkalai Biyu A Zamfara Da Abia
Description : Hukumar kula da kotuna ta kasa ( NJC) ta bayar da shawarar sallamar Alkalin Babban kotun jihar Abia, Mai Shari'a Ugbo Ononogho da kuma ...
Rating :
5