An gurfanar da wani mutum mai matsakaicin shekaru Olatubosun Soyelu gaban kotun majistri sakamakon zarginsa da ake yi da satar buhunan shinkafa 1,089 da darajarsu ya kai wuri na gugan wuri har Naira miliyan 6.5.Ana zargin mutumin ne da aikata laifin sata da hadin baki, bayan ya saci buhunan shinkafa 1,089 mallakin kamfanunuwa guda 2, Christlieb Plc da Brands Capital Ltd.
Sai dai mutumin da ake zargin ya musanta aikata laifin, daga nan sai Alkalin kotun Misi O.Martins ta bada bekinsa kan kudi naira dubu dari biyar (500,000).
Jaridar Punch ta ruwaito ana zargin Olatubosun ya aikata laifin ne a wani shago dake ‘Sura Shopping Complex’ wanda ke kan titin Simpson, jihar Legas a tsakanin wata Faburairu da watan Yuni na 2016.
Hmm….kunji su Da’u, fataken dare!
Daga Naij Hausa
Title :
Yanda Wani Yadda wani barawo ya saci buhunan Shinkafa 1,089,
Description : An gurfanar da wani mutum mai matsakaicin shekaru Olatubosun Soyelu gaban kotun majistri sakamakon zarginsa da ake yi da satar buhunan shink...
Rating :
5