Kungiyar 'yan uwa Musulmi wato 'yan Shia da ke Najeriya sun ce za su kai karar gwamnatin jihar Kaduna saboda haramta ayyukanta da ta yi.
Kakakin kungiyar, Malam Ibrahim Musa, ya shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatin jihar ta Kaduna ta dauka bai yi musu adalci ba don haka za su je kotu ne domin ta bi musu hakkinsu.
Ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin bata musu suna a idanun al'uma.
Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta amince da wasu shawarwari na wani kwamitin bincike da ta kafa bayan tashin hankalin da aka yi tsakanin sojoji da mabiya kungiyar a birnin Zaria a watan Disambar da ya wuce.
Tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar daruruwan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International.
Kazalika an kama shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da 'yan kungiyar da dama, kuma har yanzu ana ci gaba da tsare shi duk da izinin da kotu ta bayar na sakinsa.
Bbc hausa
Title :
Yan Shi’a Na Shirin Kai El-Rufai Kotu
Description : Kungiyar 'yan uwa Musulmi wato 'yan Shia da ke Najeriya sun ce za su kai karar gwamnatin jihar Kaduna saboda haramta ayyukanta da ta...
Rating :
5