TARIHIN KUBRA USMAN
Shahararriyar Mawakiyannan ta Harshen Hausa wacce akafi sani da HAJIYA KUBRA USMAN SARKIN FULANIN GOMBE
Gayanda Hirarsu Takasance da Umar Karaci N T A Hausa daga bakin ita hajiya kubra usman sarkin fulanin gombe,
NTA HAUSA: Hajiya kubra ko menene takaiceccen tarihinki?
Hajiya Kubra: Ni haifaffiyar garin Gombe ce nan jihar Gombe Nigeria,an haifeni aranar Litinin 20/2/1979.Mahaifina haifaffen wani kauyene da ake kira dabar Fulani karamar hukumar Kwami wato Malan Sidi nan Ajihar gombe,
NTA Hausa:Hajiya Kubra Koh kinyi karatu a iya tsawon rayuwarki?
Hajiya Kubra: Nayi karatu Har zuwa Matakin Secondry school,Nayi makarantar primary a "Usman Memorial Primary school Gombe" haka kuma Nayi Secondry School a "G A C (GOVERMEN ARABIC COLLGE)
NTA Hausa: Hajiya kubra fulanin gombe ko kin taba aure?
Hajiya Kubra: kwarai na taba aure wanda arayuwata da nayi na aure Allah ya albarkaceni da haihuwar yara Biyu maza bayan rabuwata da mahaifinsune na fara sana’ar waka
NTA Hausa: Awace shekara kika fara sana’ar waka?
Hajiya Kubra: Na fara waka Ashekara ta dubu biyu da bakwai (2007) inda nasamu karbuwa aduniya sanadiyar wakata ta "SARKIN FULANIN GOMBE"ashekara ta dubu biyu da tara (2009), daganan na nacigaba da rayuwata ababban birnin tarayya Abuja inda nacigaba da rera wakoki da bansan iyakarsuba kasancewar jama’a na kaunar wakokina wajen gaiyatata bikin Aure,taron Siyasa Nadin Sarauta da dai sauransu,ina Maigodiya wa Allah daya ban dumbin masoya daganan kasata najeria harma da wasu kasashe na Duniya,
NTA Hausa:Daga Karshe me zakice ga masoyanki?
Hajiya Kubra: inaiwa masoyana fatan alkhairi da fatan Allah yabar zumunci musamman wayanda ke bibiyarmu ta kafofin yanar gizo
Nagode
Takaitaccen tarihin hajiya kubra Usman sarkin fulanin Gombe wanda Umar Karaci NTA Hausa Yayi da ita Kuma yagabatar...
Title :
Tarihi Hajiya Kubra Usman (Mawakiyan Sarkin Fulanin Gombe)
Description : TARIHIN KUBRA USMAN Shahararriyar Mawakiyannan ta Harshen Hausa wacce akafi sani da HAJIYA KUBRA USMAN SARKIN FULANIN GOMBE Gayanda Hirars...
Rating :
5