Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ki bude wa mayakan Boko Haram da ke guduwa daga dajin Sambisa wuta saboda suna amfani da 'yan matan Chibok da wasu kananan yara a matsayin wata kariya ta yaki.
Manjo-Janar Lucky Irabor, wanda ke jagorantar yakin da sojoji ke yi da kungiyar ya nuna wa manema labarai wani faifan bidiyo da yace an dauka a lokacin da ake kai hari a dajin Sambisa, inda aka hasko mayakan Boko Haram na tafiya tare da mata da kananan yara.
"Da alamu hakan na nuna yadda suke amfani da su domin neman kariya, kuma shi ne dalilin da ya sanya sojojin ba su bude musu wuta ba".
Rundunar sojin ta kuma ce ta gano al-Kur'anin da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya ke karantawa a lokacin da ta fattataki mayakan kungiyar daga sansaninsu na karshe a dajin.
Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na jami'an tsaron. Kuma rundunar sojin ba ta fitar da hoton al-Kur'anin ba kawo yanzu.
Janar Irabor ya kara da cewa ''Mun yi amanna shiga dajin zai taimaka wajen gano sauran 'yan matan na Chibok da har yanzu mayakan ke tsare da su.
Abin da ba mu tabbatar ba shi ne ko matan nan da suke tare da su 'yan matan Chibok din ne ko kuma a'a,'' in ji shi.
Jami'an tsaron sun kuma ce sun kama wasu da ake zargi 'yan Boko Haram ne su 1,240, a lokacin da suke fatattakar mayakan daga dajin.
Mutum 413 daga cikin wadanda ake zargin maza ne manya, sannan 323 manyan mata ne, sai yara maza 251 da kuma yara mata 253.
Ya ce, "Muna yi masu tambayoyi, domin mu tabbatar ko 'yan Boko Haram ne, saboda mun san babu yadda za a yi wani da baya cikin kungiyar Boko Haram, ya zamana yana cikin dajin na Sambisa."
A watan Afrilun 2014 ne Boko Haram ta sace 'yan matan fiye da 200 daga makarantarsu a garin Chibok na jihar Borno. Baya ga su, kungiyar ta kuma sace dubban mata da maza, da ma kananan yara.
Akalla mutum 30,000 ne suka mutu a shekara bakwan da aka shafe anan rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kimanin mutum 100,000, yawancinsu yara kanana, ka iya mutuwa saboda yunwa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
Daga BBCHAUSA
Title :
Sojojin Najeria Sun Sami Al-Kur'anin Shekau a Sambisa
Description : Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ki bude wa mayakan Boko Haram da ke guduwa daga dajin Sambisa wuta saboda suna amfani da 'yan matan C...
Rating :
5