DAGA Rariya
Shugaban Gambia mai barin gado, Yahya Jammeh ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar wanda da farko ya amince da shan kaye.
Yahya Jammeh ya sha kaye daga abokin takararsa, Adama Barrow, bayan da ya samu kaso 45 na kuri'ar da aka kada.
A makon da ya gabata ne dai Yahya ya amince shan kaye, a inda ya kira abokin takarar tasa, Adama Barrow, domin taya shi murna.
Jameh ya ce ya janye matsayinsa na farko ne bayan la'akari da cewa ba a kidaya kuri'ar daidai ba.
Ya kuma kara da cewa shi ne mutumin da ya lashe zaben da fifikon kuri'a dubu 87.
A 1994 dai Yahya Jameh ya hau mulkin kasar, bayan juyin mulkin da ya jagoranta a kasar.
Title :
Shugaban Kasar Gambiya Ya Ki Amincewa Da Sakamakon Zabe
Description : DAGA Rariya Shugaban Gambia mai barin gado, Yahya Jammeh ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar wanda da farko ya amince da shan ka...
Rating :
5