A wani zama na awanni shida da majalisar zartarwar kasa ta yi a jiya Laraba karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, majalisar ta aminta da kasafin kudin shekarar 2017 wanda jimilar kudaden da za a kashe wajen gudanar da ayyukan raya kasa da sauran abubuwa ya kai Naira tiriliyan 7.2
Wannan adadi ya nuna cewa kasafin na shekarar 2017 ya haura na shekarar bana wanda ke da jimilar kudi Naira tiriliyan 6.06 da kaso 24 cikin 10
Ministan Kasafin Kudi Da Tsare-Tsare, Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai mika wannan kasafi ga majalisa don dubawa kuma daga nan majalisar za ta duba ta ga lokacin da ya dace ta kira shugaba Buhari don gabatar da kasafin a gabanta
Haka kuma Mista Udoma ya bayyana cewa takardar da fadar shugaban kasa ta aikewa da majalisa na bukatar sahale mata karbar bashi don aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa na dauke da bayanai cikakku kuma gamsassu akasin yadda majalisar ta bayyanawa manema labarai
Ministan ya ci gaba da cewa, takardar neman bashin manyan ayyukan shekarar 2017 zuwa 2019 da muka aikawa majalisa ya samu kulawar aiki daga kwararru, saboda haka takardar ta fi karfin a ce mata ba ta dauke da bayanai
Source Al'ummata.com
Title :
Shugaba Buhari Ya Shirya Kasafin Kudin 2017 Na Naira Tiriliyan 7.2
Description : A wani zama na awanni shida da majalisar zartarwar kasa ta yi a jiya Laraba karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, majalisar ta amin...
Rating :
5