Rahotanni sun nuna cewa ana hasashen Shugaba Buhari ba zai sake tura wa Majalisar tarayya suna Ibrahim Magu don tabbatar da shi Shugaban hukumar EFCC a maimakon haka, ana hasashen za a maye gurbinsa da tsohon Shugaban Hukumar, Nuhu Ribadu ko kuma Shugaban Kwastan Na Kasa, Hamid Ali.
Wata majiya mai karfi ta nuna cewa 'yan Siyasar da ke adawa da nadin Ibrahim Magu na ci gaba da lalubo kwararrun da za su maye gurbinsa wanda ya hada har da tsohon Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda, Amodu Ali wanda a halin yanzu shi ke binciken badakalar Halliburton wadda ta shafi wasu tsoffin shugabannin kasa. A cewar majiyar, masu adawa da Magu na shirin garzaya wa kotu idan har Shugaba Buhari ya sake tura sunan Magu ga majalisa.
Rariya
Title :
Ribadu Ko Hamid Ali Za Su Maye Gurbin Magu A EFCC
Description : Rahotanni sun nuna cewa ana hasashen Shugaba Buhari ba zai sake tura wa Majalisar tarayya suna Ibrahim Magu don tabbatar da shi Shugaban hu...
Rating :
5