Akalla mutum 60 ne suka mutu bayan da wani ginin coci ya rufta ranar Asabar a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.
Rahotanni sun ce ginin na majami'ar Reigners Bible Church ya rufta ne a lokacin da ake bikin nada shugabanta a matsayin Bishop.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da jaje tare da ta'aziyya ga al'ummar jihar.
Gwamnan jihar Udom Emmanuel na cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, kuma Shugaba Buhari ya taya shi murna kan kubutar da ya yi.
Mista Emmanuel ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nemi al'umma da su agazawa mutanen da suka jikkata a hadarin.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato wadanda suka shaida lamarin na cewa ana kan yi wa ginin kwaskwarima saboda hasashen cewa jama'a da dama za su halacci taron.Wani ganau ya ce "Ana cikin bikin nada Fasto Akan Week kwatsam sai ginin ya rufta baki daya".
Ya kara da cewa "Mutane da dama sun makale a kuraguzan ginin a daidai lokacin da masu aikin ceto ke cigaba da kai dauki."
Shafin labarai na Premium Times ya ce an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa asibitoci da dama a fadin birnin.
Ana yawan samun ruftawar gine-gine a Najeriya, abin da masu sharhi ke alakanta wa da rashin bin doka da amfani da kayan aiki marasa kyau.
Akalla mutum 115 ne suka mutu a watan Satumbar 2014 lokacin da wani gini mallakar Cocin Fasto TB Joshua ya rufta a birnin Lagos.
Daga BBCHAUSA
Title :
Photos: Wani Ginin Coci Ya Kashe 'Mutane 60' A Akwa Ibom
Description : Akalla mutum 60 ne suka mutu bayan da wani ginin coci ya rufta ranar Asabar a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya. Rahotanni ...
Rating :
5