Yayin da ake ci gaba da shagalin bikin ‘yar sa, a yau 17 ga watan Disamba shugaba kasa Buhari ya cika shekaru 74 a duniya.
Tun a jiya ‘yan Nijeriya ke taya shugaban murnar, tare da addua’r Allah ya sanya alkhairi a bikin ‘yar ta sa wanda aka yi a jiya Juma’a, sai dai kuma da yawa sun yi amfani da damar wajen janyo hankalinsa ga halin matsi da kuncin rayuwa da ‘yan kasar ke ciki.
A jiyan ne dai aka shafa fatiha tsakanin ‘yar shugaban kasar, Zahra da Ahmed Indimi, da ga biloniyan dan kasuwan nan Muhammad Indimi
Yayin da manyan jami’an gwamnati kamar su kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, suka fitar da sakonnin yi wa shugaban murnar zagayowar ranar haihuwar sa suka kuma yi masa addu’ar karin lafiya, talakawan Nijeriya sun yi amfani da shafukan sada zumunta kamar su Facebook inda suka bar sakonninsu a shafin uwar gidan shugaban kasar Aisha Buhari da ke taya Zahra Murna, da kuma korafi akan halin da kasar ke ciki.
A sakon da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa Turaki Hassan, Dogara ya bayyana mulkin Buhari a matsayin nufi na Allah, inda ya kara da cewa ‘yan Nijeriya na ci gaba da imanin cewa zai gyara kasar ta yadda kowa zai ji dadin ta a nan gaba.
Al'ummata.com
Title :
Photos: Daga Wajen Bikin Murna Ranar Haihuwa Shugaba Muhammadu Buhari
Description : Yayin da ake ci gaba da shagalin bikin ‘yar sa, a yau 17 ga watan Disamba shugaba kasa Buhari ya cika shekaru 74 a duniya. Tun a jiya ‘yan ...
Rating :
5