Bayan auren Zahra Buhari jama'ar Nijeriya hankulansu ya karkata zuwa ga Hannatu Muhammad Buhari wadda ita ma 'ya ce ga shugaban kasa Buhari.
Saidai abin mamakin shine yadda yanzu 'yan social media suke ta kirkire-kirkiren account na Facebook da sunan Hanan Muhammad Buhari din saboda tsabar iya 419.
Kafin auren Zahra buhari ba kowa bane ya san Hanan. Haka ya sa ba za ka taba ganin wani shafi na account nata a social media ba.
Amma yanzu kuwa tunda aka nunata a jaridu nake ta ganin account mai suna Hannan Buhari yana yawo a yanar gizo wai Hannah Buhari.
To Allah ya kyauta. Ya kamata jama'a su daina neman suna da sunan wani. Yin hakan babban kuskure ne domin yana da kyau ka tsaya inda Allah ya ajiye ka.
To Wallahi Hannatu ta ce ba ta da wani account da sunan mahaifinta a shafin social media. Amma tace tana chat ba kuma lallai bane a san Username dinta
Da fatan za a kiyaye a kuma kula da 'yan 419.
Daga Rariya
Title :
Photos: Ba Ni Da 'Account A Shafin Social Media' - Hanan Buhari
Description : Bayan auren Zahra Buhari jama'ar Nijeriya hankulansu ya karkata zuwa ga Hannatu Muhammad Buhari wadda ita ma 'ya ce ga shugaban kasa...
Rating :
5