Karya Buhari Yake Yi, Muna Nan A Raye, Kamar Yadda Shekau Ya Bayyana A Sabon Bidiyon Da Ya Fitar A Yau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana a wani faifan bidiyo inda ya musanta ikirarin Shugaba Muhammadu Buhari cewa sojoji sun kore su daga dajin Sambisa.
"Muna nan daranmu da lafiyarmu. Babu wanda ya kore mu daga wani wuri," in ji Shekau, wanda ya bayyana a bidiyon zagaye da wasu mayaka dauke da manyan bindigogi.
Kamfanin dillancin labarai na AFP yace a bidiyon na tsawon minti 25, Shekau ya ce "babu wanda zai iya sanin inda suke har sai idan Allah ya so hakan ya faru".
A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya ce sojojin kasar sun fatattaki mayakan daga dandalinsu na karshe a dajin na Sambisa.
Kawo yanzu rundunar sojin kasar ba ta ce komai ba game da wannan bidiyo, wanda aka fitar a yau Alhamis.
Daga Rariya
Title :
Muna Nan A Raye - Abubakar Shekau
Description : Karya Buhari Yake Yi, Muna Nan A Raye, Kamar Yadda Shekau Ya Bayyana A Sabon Bidiyon Da Ya Fitar A Yau Shugaban kungiyar Boko Haram Abubaka...
Rating :
5