DAGA ISMAIL AHMAD YALWA NGURU
Majalisar ta gayyaci Abdulmummuni Jibrin ya zo majalisar ya kare kansa bisa ga laifuka biyun da majalisar ke zargin ya aikata.
Majalisar ta zarge shi da laifuka biyu, wato rashin zuwa aiki da kuma wai yana aiki da asusun banki na kasashen waje.
Daya cikin 'yan majalisar Timothy Ngolu ya nuna suna da hujjar gayyatar shi Jibrin saboda wai su masu jin kukan mutane ne. Wajibi ne su kira shi su bayyana masa abubuwan da suke zargins hi da yi da kuma korafe korafen da suka samu a kansa. Ngolu yace dole ne su ji daga bakinsa.
Akan cewa Abdulmummuni Jibrin ya daina zuwa majalisar ne saboda majalisar ce ta kore shi sai Timothy Ngolu ya musanta batun. Yace akwai doka akan zuwa majalisa kuma wanda yaki kotu na iya yin waje da shi daga majalisar.
Shi ma Yuguda Hassan Kila mai wakiltar mazabar Gwaram jihar Jigawa yace matakin da majalisar ta dauka na son jin ta bakin Abdulmummuni Jibrin shi ne adalci. Suna bukatan su yi masa tambayoyi idan shi kuma yana da tambayoyi sai yayi masu.
Shi dai Abdulmummuni yayi alkawarin bayyana a gaban majalisar idan ya samu wasika a hukumance.
Title :
Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi
Description : DAGA ISMAIL AHMAD YALWA NGURU Majalisar ta gayyaci Abdulmummuni Jibrin ya zo majalisar ya kare kansa bisa ga laifuka biyun da majalisar ke...
Rating :
5