Majalisar Dattawa ta ki amincewa da nadin Ibrahim Magu a matsayin sabon Shugaban hukumar EFCC bayan ya jima a matsayin Shugaba na riko.
D yake tabbatar da matsayin majalisar, Mai Magana da Yawun Majalisar, Sanata Sabi Abdullahi ya nuna cewa majalisar ta yanke shawarar ce saboda wasu bayanan tsaro da suka samu game da Ibrahim Magu.
Tun a makon da ya gabata ne, aka sa ran majalisar za ta tantance Ibrahim Magu a matsayin sabon Shugaban EFCC amma kuma aka dage zuwa wannan mako, lamarin da wasu suka yi hasashen cewa akwai matsala musamman yadda tun farko wasu sanatocin da ake tuhuma da rashawa suka nuna rashin aminta da Magu
Title :
Majalisa Ta Ki Tantance Magu A Matsayin Shugaban EFCC
Description : Majalisar Dattawa ta ki amincewa da nadin Ibrahim Magu a matsayin sabon Shugaban hukumar EFCC bayan ya jima a matsayin Shugaba na riko. D ...
Rating :
5