a ...wasu daga cikin 'yan wasa, makada da mawakan da suka haska a bikin
A yau Juma'a ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aurar da 'yarsa Zahara ga Ahmed Mohammed Indimi akan zinari 12 wanda darajarsu ya kai naira 250,000, a matsayin sadaki.
Mataimakin babban limamin babban masallacin Abuja, Sheikh Ibrahim Makari ne ya jagoranci daura auren bayan kammala sallar Juma'a.
Majiyarmu ta samu bayanin cewa Sarkin Fulanin Daura, Alhaji Yusuf Sani ne ya bayar da auren Zahra a madadin iyalin Buhari.
Daga cikin manyan mutane da suka halarci daurin auren sun hada da tsohon Gwamnan jihar Lagos, Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, da shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Cif Bisi Akande.
Gwamnonin da suka halarci daurin auren sun hada da, Rauf Aregbesola, da Nasir El-rufai, da Umaru Almakura, da Yahaya Bello da Aminu Masari, da dai sauransu.
..Fitattun 'yan wansan da suka halarci bikin
1. Darey Art Alade
Shine ya shirya kwallon bikin Zahra da Ahmed
2. Ayo Makun aka AY
Dan wasan barkwancin kamar Darey Art Alade shi ma ya samu damar halartan bikin Zahra da Ahmed.
3. Adekunle Gold
Mawakin YBNL ya samu halartan bikin inda ya yi wasu daga cikin wakokinsa.
Dangantakar dake tsakanin Zahra Buhari da Adekunle Gold ya wuce na masana’atar nishadantarwa kamar yadda su biyun sun kasance abokan juna tun ma kafin shugaba Buhari ya hau mulki a 2015. Su dukka biyun sun kasance masu goyon bayan masu cutar sikila. Sun kuma kasance jakadun gidauniyar ta Sickle Cell Aid Foundation (SCAF) a Nijeriya.
4. Kiss D
Shi ma ya yi wasa a gurin taron
5. Seyi Shay
Bayan wasa da tayi a gurin bikin Ahmed da Zahra, Seyi Shay ta fito cikin kyakyyawar shiga a gurin taron.
6. Di’Ja
Ya kasance abu mai sauki kasancewar Di’ja a cikin jerin mawakan da suka yi wasa a gurin taron kamar yadda ta kasance 'yar Arewa kuma tana da masoya a gurin.
7. DJ Jimmy Jatt
Makidi (DJ) mafi shahara a Nijeriya ya kasance wanda aka dauko na musamman don kida a gurin taron.
8. Comedian Senator
Comedian Senator
Ya halarci gurin inda ya nishadantar da jama’a sosai a gurin taron.
9. Fati Nijar
Haka ita ma shahararriyar zabiyar nan Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar tana daga cikin mawakan da suka gavatar da wasa a shagulgulan bikin da aka gudanar
Daga Rariya
Title :
Kimanin Naira Dubu 250 Aka Biya Sadakin Zahara Buhari
Description : a ...wasu daga cikin 'yan wasa, makada da mawakan da suka haska a bikin A yau Juma'a ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aurar da ...
Rating :
5