Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa ta dauki matakin gaggawa kan tashin farashin kayayyakin abinci inda ta haramta wa 'yan kasuwa boye abinci da kuma haramta ayyukan dillanci a kan kayayyakin abinci.
Shugaban. Karamar Hukumar Aminu Ibrahim ya nuna cewa hukumar ta dauki matakin ne saboda yadda 'yan kasuwa ke haddasa ta tashin farashin kayayyakin abinci da gangan.
Ya ce an kafa kwamitin mutum 15 da ya kunshi sarakunan, jami'an tsaro, malamai da masu ruwa da tsaki kan harkar wanda aka dora masu nauyin sa Ido kan yadda 'yan kasuwa ke tafiyar da harkokinsu.
Daga Rariya
Title :
Karamar Hukumar Sokoto Ta Haramta Wa 'Yan Kasuwa Boye Kayayyaki Abinci
Description : Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa ta dauki matakin gaggawa kan tashin farashin kayayyakin abinci inda ta haramta wa 'yan kasuwa boye abin...
Rating :
5