Wani rahoto da ya ke fitowa daga jaridar Vanguard ya bayyana cewa sabuwar jam’iyyar nan ta hadaka tsakanin wasu jigajigan ‘yan jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ake batun za a kafa a shekara mai zuwa za a yi mata lakabi ne da ADP
Rahoton na nuna cewa, masu rajin kafa wannan sabuwar jam’iyya daga sassan kasar nan shida za su hadu a Abuja a ranar 19 ga watan Disamba, 2016 don radawa sabuwar jam’iyyar suna
Rahoton ya yi nuna da cewa a cikin jerin sunayen da ake shawarar radawa jam’iyyar, sunan ADP da ke da ma’anar Action Democratic Party ya fi samun karbuwa.
Da zarar an kammala batun radin suna, majiyarmu ta bayyana mana cewa sabuwar jam’iyyar za ta mika takardun yi mata rijista ga hukumar zabe ta kasa INEC don zama cikakkiyar jam’iyya
daga alummata.com
Title :
Jiga-jigan APC Da Na PDP Za Su Kafa Jam’iyyar ADP
Description : Wani rahoto da ya ke fitowa daga jaridar Vanguard ya bayyana cewa sabuwar jam’iyyar nan ta hadaka tsakanin wasu jigajigan ‘yan jam’iyya mai ...
Rating :
5