'Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S (Jesus) ya yi wa mabiyansa albishir da zuwan Annabin karshe mai suna Muhammad (Annabi Muhammadu S.A.W).
An yi ittifakin cewa Littafin ya kai shekara 1,500 da rubutawa. Kuma an rubuta shi ne da ruwan zinari a cikin harshen "Aramaic" (Larabci).
Jaridar Daily Mail ta Amerika ta ruwaito cewa, gano littafin wanda aka yi hasashen duk falle daya a cikinsa zai kai kimanin Yuro milyan £14 ya jawo muhawara mai tsanani a tsakanin mabiya darikar Vatican da musulmi inda har Fafaroma Pope Benedict XVI ya nemi a kawo masa bibile din ya gani.
Idan dai aka tabbatar da zargin da ake yi akan Bible din kuma ta tabbata haka din ne. To akwai chakwakiya ganin cewa littafin zai karyata mabiya addinin kirista dake Allantar da Isah (AS) da kuma masu cewa Jesus din dan Allah ne. Bible din zai tabbatar da cewa addinin Islama shine gaskiya kuma Musulmai sune ke kan addini na gaskiya wanda (Almasihu/Jesus) ya umurci mabiyansa akai.
Majiyar ta mu ta kuma ruwaito cewa an gano littafin ne tun a shekara ta 2000 amma hukumomin kasar Turkiyya suka cigaba da tsaron shi har zuwa shekara ta 2012 inda suka kaishi gidan tarihi na Ankara Ethnography Museum. Kuma ana sa ran nan bada jimawa ba za'a rika nunawa mutane Bible din a gidan tarihin kasar.
Ministan raya Al'adu da yawon bude ido na kasar Turkiyya, Ertugrul Gunay ya ce suna kyautata zaton Bible din na gaskiya ne shi yasa wasu suka boye shi saboda yadda littafin ya yi bayani akan ainihin matsyin Almasihu (Jesus) sabanin tunaninsu.
Jaridar ta daily mail ta kara da cewa hankalin fafaroma da sauran manyan limaman kiristoci ya tashi sakamakon gano wannan littafi na Bible.
DAGA HAUSA TIMES
Title :
Hankalin Fafaroma Ya Tashi Sakamakon Gano Wani Bible Da 'Jesus' Ke Wasiyyan Zuwan Annabi Muhammadu (S.A.W)
Description : 'Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S (Jesus) ...
Rating :
5