* Buhari Zai Ci gaba Da Rarrashin Shugaba Jammeh
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa dole Shugaban Gambiya mai barin Gado, Yahya Jammeh ya mutunta ra'ayin 'yan kasar ta hanyar mika mulki ga zababben shugaban kasar, Adama Barrow.
Haka nan kuma shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da shugabantar ƙokarin sasanta rikicin siyasar ƙasar Gambia duk da sukar ƙokarin shiga tsakanin da shugaba Yahya Jammeh ya yi.
A ranar Talata ne shugaba Jammeh ya ce ƙokarin shiga tsakanin da kungiyar ECOWAS ke yi ƙarkashin jagorancin shugaba Buhari katsalandan ne a cikin harkokin cikin gida na ƙasar sa.
Sai dai mai magana da yawun fadar shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu ya ce shugaban ba zai ja da baya ba wajen sauke nauyin da aka ɗora masa na warware taƙaddamar cikin lumana.
Hakan na zuwa ne bayan da kotun ƙoli a Gambia, ta ce za ta saurari ƙarar da shugaba Yahya Jammeh ya shigar a gabanta inda yake ƙalubalantar sakamakon zaben shugaban ƙasa da aka yi a watan Disamba.
Babban alƙalin kotun Emmanuel Fagbele, ya ce an naɗa alƙalai daga Najeriya da Saliyo wadanda za su kasance cikin alƙalan da za su saurari ƙarar amma har yanzu basu iso ba, kuma sai a watan Janairu ne za ta soma sauraron ƙarar saboda ƙarancin alƙalai.
A bara ne dai shugaba Jammeh ya kori da dama daga cikin alƙalan kotun ƙolin bayan da suka sassauta hukuncin kisa da aka yanke wa wasu fursunoni zuwa ɗaurin rai da rai.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi Mista Jammeh da cin zarafin masu adawa da gwamnatin sa, a lokacin da ya shafe shekaru 22 yana mulkin ƙasar Gambia.
Rariya
Title :
Dole Shugaba Jammeh Na Gambiya Ya Mika Mulki - Majalisar Dinkin Duniya
Description : * Buhari Zai Ci gaba Da Rarrashin Shugaba Jammeh Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa dole Shugaban Gambiya mai barin...
Rating :
5