Rahotanni sun tabbatar da cewa majalisar Dattawa ta ki tantance Ibrahim. Magu a matsayin Shugaban hukumar EFCC ne sakamakon wani rahoto da ta samu daga jami'an rundunar tsaro na farin kaya (DSS) wanda ya nuna cewa Magu bai cancanci jagorantar hukumar ba.
Rahoton mai dauke da sa hannun Mista Folashade Bello a madadin Shugaban DSS, Lawal Daura wanda aka aika majalisar a ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 2016 ya nuna cewa Ibrahin Magu na zaune ne a wani gidan haya da kudinsa ya kai milyan 40 wanda kuma wani dan kasuwa ne ke biyan kudaden a maimakon hukumar EFCC
Haka nan kuma, rahoton ya nuna cewa. Magu ya nemi hukumar raya birnin Abuja ta gyara masa gidan wanda kuma aka ba dan kasuwar da ke biyan kudin hayar kwangilar aikin a kan kudi Naira milyan 43 sannan kuma rahoton ya nuna yadda Magu ke amfani da jirgin saman dan kasuwar wajen yin tafiye tafiye.
Daga Rariya
Title :
Dalilin Da Ya Sa Majalisa Ta Ki Tantance Magu A Matsayin Shugaban EFCC
Description : Rahotanni sun tabbatar da cewa majalisar Dattawa ta ki tantance Ibrahim. Magu a matsayin Shugaban hukumar EFCC ne sakamakon wani rahoto da...
Rating :
5