Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya taya zababben Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow murnar lashe zabe sannan kuma ya yaba wa Shugaba Mai barin Gado bisa dattakon da ya nuna na amincewa da sakamakon zaben.
A nasa bangare, Shugaban kasar Gambia mai jiran gado, Adama Barrow, ya ce, idan har akwai yiwuwar gurfanar da shugaban kasar mai barin gado, Yahya Jammeh, to za a bi ka'ida wajen hakan.
Adama Barrow ne dai ya kayar da Yahya Jammeh da tazarar kuri'a fiye da 50,000.
Mutane suna ta yin kira da a gurfanar da Yahya Jammeh bisa ayyukan take hakkin jama'a da ake zargin ya aikata.
Rariya
Title :
Buhari Ya Taya Zababben Shugaban Gambiya Murnar Lashe Zabe
Description : Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya taya zababben Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow murnar lashe zabe sannan kuma ya yaba wa Shugaba Mai b...
Rating :
5