Canjin Yanayi Ya Sanya Shugaba Buhari Sake Dage Ziyarar Da Ya So Kawowa Jihar Bauchi A Yau
Sakamakon canjin yanayi da aka tashi da shi a safiyar yau a Abuja ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari sake dage ziyarar aiki na kwana daya da ya so kawowa jihar Bauchi a yau.
A yayin ziyarar da shugaba Buhari zai kawo, zai bude sabon aisibitin da aka gina ne a sansanin sojojin sama da sauran wasu ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi ta yi.
Saidai a wani jawabi da shugaban kasar ya fitar, ya bayyana cewa ya dage ziyarar ne sakamakon tashi da hazo da aka yi a safiyar yau wanda hakan ya sa jirgi ba zai samu damar tashi ba.
A yayin tattaunawa da manema labarai, gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa za su sake sanya ranar da shugaban kasar zai kawo ziyarar. Gwamnan ya kuma godewa al'ummar jihar Bauchi bisa ga yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu suna jiran isowar shugaban kasan.
Kafin bayyana dage ziyarar, tuni al'ummar jihar Bauchi da suka shirya tsaf domin tarbar shugaban kasan. Haka ma wasu daga cikin mukarraban shugaban kasa har sun isa jihar ta Bauchi inda suke jiran isowarsa. Daga cikin su akwai mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafun yada labarai, Bashir Ahmad da sauransu.
Title :
Buhari Ya Sake Dage Ziyarar Da Ya Kawowa Jihar Bauchi Yau
Description : Canjin Yanayi Ya Sanya Shugaba Buhari Sake Dage Ziyarar Da Ya So Kawowa Jihar Bauchi A Yau Sakamakon canjin yanayi da aka tashi da shi a sa...
Rating :
5