Farfesa Ango Abdullahi daya daga cikin Dattawan Arewa ya ce Shugaban kasa Buhari ya fi ffita Kudancin kasar nan fiye da Arewa inda ya fito.
Ango ya ce duk da cewar 'yan Arewa su suka fi zaben Buhari amma ba ya canja Arewa kamar yadda yake canja Kudancin kasar nan.
Ango Abdullahi ya fadi hakan ne a gidan rediyon Liberty dake Kaduna, kuma ya ce sam sam wannan Gwamnatin ta Buhari ba ta wakiltar arewa yadda ya kamata.
Bayan haka Ango Abdullahi ya ce shugaba Buhari bai taimakawa Arewa da manyan aiyuka ba a cikin kasafin kudin 2016 kamar yadda ya kamata.
.
Ango Abdullahi yace 'yan Arewa ne suka zabi Buhari ba wai dan ya kasance a jam'iyyar APC ba, sun zabe shi ne dan su kawar da mulkin Jonathan sakamakon karya yarjejeniyar shekarar 1999.
.
Daga Rariya
Title :
Buhari Ya Fi Fifita Yankin Kudu Fiye Da Na Arewa, Inji Farfesa Ango Abdullahi
Description : Farfesa Ango Abdullahi daya daga cikin Dattawan Arewa ya ce Shugaban kasa Buhari ya fi ffita Kudancin kasar nan fiye da Arewa inda ya fito....
Rating :
5