Wata majiya a gwamnatin Najeriya ta shaida wa BBC cewa Shugaba Muhammadu Buhari da wasu shugabannin Afirka ta Yamma za su ziyarci Gambia a ranar Talata a wani yunkuri na sasanta rikicin siyasar kasar.
An shiga rudani ne bayan da Shugaba Yahya Jammeh ya ki yarda da shan kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Majiyar ta ce shugabannin za su gana da Mista Jammeh domin su shawo kansa a kan ya mutunta alkawarin da ya yi tun farko na mika mulki.
Dan kasuwa mai hada-hadar gidaje Adama Barrow ne ya doke Mista Jammeh a zaben na ranar 1 ga watan Dismba.
Haka kuma tawagar za ta gana da zababben shugaban kasar wanda ya ce rayuwarsa na cikin hadari.
Sannan ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan Mista Jammeh ya sauka daga kan mulki ba tare da bata lokaci ba.
Rahotanni sun ce Mista Barrow ya yi maraba da tawagar, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shi yana cewa.AFP ya kuma ce ba ya ga Shugaba Muhammadu Buhari, tawagar za kuma ta kunshi Shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf da wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Mohamed Ibn Chambas.
Ana kuma sa ran Shugaban Ghana John Mahama shi ma zai halarta.
Sakamakon zaben da hukuma ta bayyana ya nuna cewa:
Mista Barrow ya samu kuri'u 222,708 kashi (43.3%)
Mista Jammeh ya samu 208,487 kashi (39.6%)
Yayin da dan takara na uku, Mama Kandeh, ya samu 89,768 kashi (17.1%)
Daga BBCHAUSA
Title :
Buhari Na Shirin Sasanta Rikicin Gambia
Description : Wata majiya a gwamnatin Najeriya ta shaida wa BBC cewa Shugaba Muhammadu Buhari da wasu shugabannin Afirka ta Yamma za su ziyarci Gambia a r...
Rating :
5