Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga iyalan yan bautar kasa (NYSC) guda uku da suka rasa rayukansu a sansanin yan bautar kasa a jihohi uku.
A cewar wani rubutu daga Femi Adesina, mataimakin shugaban kasa na musamman a kafofin watsa labarai, Buhari ya bayyana mutuwar wadannan matasa yan Najeriya a matsayin “al’ajabi, bakin ciki da kuma bazata.”
Shugaban kasa yace yay i bakin cikin mutuwarsu cewa sun mutu a halin amsa kiran bautar kasa.
Ya yi kira ga yan uwa, abokai da kuma mataimakan marigayin da su amsa ta’aziyar da tare da sanin cewa masoyan nasu sun biya farashi mai girma a yayin bauta wa kasa ba wai a dalili mara tushe ba.Shugaban kasa Buhari ya kara da yin ta’aziyya ga Darakta Janar da ma’aikatan NYSC kan mutuwar yan bautar kasa, Chinyerum Nwenenda Elechi, Ifedolapo Oladepo da kuma Monday Asuquo Ukeme, a Jihar Bayelsa, Kano da kuma Zamfara.
Yayinda ya bukaci ma’aikatan da suyi duk abunda zasu iya da zarfin su gurin kare rayukan wadanda ke a karkashin ikon su, shugaban kasa ya yi kira ga iyaye da wakilan yan bautan kasa da karda su yi tashin hankali kana bun bakin ciki da ya afku.
A kan mutuwar Miss Ifedolapo Oladepo a jihar Kano, shugaban kasa ya bada umurnin bincike domin gano gaskiyar Magana.
Ya yi addu’a ga mamatan kan Allah Ubangiji ya kansu.
Title :
Buhari Bayar Da Umurnin Da Bincike Mutuwar Yan Bautar Kasa
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga iyalan yan bautar kasa (NYSC) guda uku da suka rasa rayukansu a sansanin yan bautar kasa a ...
Rating :
5