Malam Uba Sani ya bayyana abunda ya haddasa babban gaba a tsakanin tsohon ubangidansa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Malam Nasir el-Rufa’I, wanda a karkashinsa yake aiki yanzu a matsayin mai basa shawara a harkan siyasa.
Mataimakin na gwamnan jihar Kaduna, a wani hiransa da yan jaridu a Abuja, yace El-Rufai mutun ne mai gaskiya kuma cewa wannan ya sa yana da masoya da kuma makiya da yawa.
Sani ya bayyana cewa a baya, “kokarin ganin ya dukufar da el-Rufai ta ko halin ‘ka’ka ya kasance abu mafi soyuwa ga Atiku. Amma a matsayin mutane masu hikima, zamu iya cinkar dalilin da yasa yake yawan kai hari ga gwamnan a kai-a kai.
Mataimakin gwamnan ya yi jayayya cewa Mallam el Rufai bai taba kasancewa mamba na tawagar yan rashawa ba.
Na karanta hirar Alhaji Atiku da aka buga a majullar Zero Tolerance, wanda babu shakka aka kuma buga su a dandamalin watsa labarai daban-daban.
A cewar Sani, “Bajintar Mallam el Rufai a dukkan mukaman da ya rike sanannu ne kuma an ajiyesu yanda ya dace. Yaki da rashawarsa na saka shi cikin hatsari a ko yaushe.
El-Rufai da muka sani ba zai taba karya doka ko a kan kansa ba. Imma a inda yayi aiki a matsayin Darakta Janar na tsawon shekaru hudu; ko kuma a ma’aikatar babban birnin tarayya, inda yayi shugabanci a matsayin minister na wani shekaru hudun; har ma a jihar Kaduna inda yake a matsayin gwamna mai ci, yaki da cin hancin el-Rufai mai dorewa ne."
naij Hausa
Title :
Atiku Na Harin El-Rufai Saboda Shi Mai Gaskiya Ne - Uba Sani
Description : Malam Uba Sani ya bayyana abunda ya haddasa babban gaba a tsakanin tsohon ubangidansa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Mal...
Rating :
5