* Magu Ya Wanke Kansa Bisa Umarnin Ministan Shari'a
Wata majiya daga jaridar ' The Nation' ta nuna cewa akwai hannun wasu gwamnoni bakwai wajen kintsa makarkashiyar da majalisa ta ki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban hukumar EFCC.
A cewar majiyar, gwamnoni uku sun fito ne daga yankin Kudu maso Kudu sai biyu daga yankin Yarbawa, biyu kuma daga yankin Arewa sai Gwamnan daya daga yankin Kudu maso Gabas. Sai kuma wasu tsoffin gwamnoni da ministoci wadanda suka yi alwashin ganin ba a tabbatar wa Magu da kujerar shugabancin EFCC ba.
Sai dai kuma majiyar ta nuna cewa akwai wasu gwamnoni daga Arewa wadanda suka marawa Magu baya. Tuni dai, Ibrahim Magu ya wanke kansa daga zarge zargen da hukumar tsaro na farin kaya ta gabatar a kansa bayan bisa umarnin Ministan Shari'a, Abubakar Malami wanda ya ba shi Awowi 48 don yin hakan kuma ana sa ran za a mika wa Buhari rahoton don daukar matakin da ya dace.
Title :
Ana Zargin Wasu Gwamnoni Bakwai Da Makarkashiyar Kin Amincewa Da Magu
Description : * Magu Ya Wanke Kansa Bisa Umarnin Ministan Shari'a Wata majiya daga jaridar ' The Nation' ta nuna cewa akwai hannun wasu gwam...
Rating :
5