Jaridar Daily Mail ta rahoto cewa ana yunkurin hana amfani da dogon Hijabi da ake kira burqah a Kasar Jamus. Shugaban Kasar Jamus, Angela Merkel tace bai dace ace ana amfani da burqah a Kasar Jamus ba damin Kasar Kirista ce.
Shugaban Kasar Jamus, Angela Merkel tace Jamus Kasar Kirista ce don haka bai dace ace ana amfani da dogon Hijabi ba watau burqah. Shugaban Kasar ta bayyana haka ne a wajen wani Taron Jam’iyyar su ta CDU da aka gudanar.
Shugaban Kasar tace za tayi kokarin hana Musulmai dindirinzo zuwa Kasar Jamus din. Tace ba za a maimaita irin abin da ya faru a Kasar ba shekarar bara lokacin da Musulmai suka yi ta Hijira suna shigowa Kasar.
Jam’iyyar CDU ta su Angela Merkel ta fadi zaben Jihohi da aka yi saboda matsayar ta game da Musulmai da suke shigowa Kasar. Kusan Musulmai 890,000 suka shigo Kasar Jamus da ke Tsakiyar Turai shekarar bara.
Naij Hausa
Title :
Ana Shirin Hana Amfani Da Hijabi A Jamus
Description : Jaridar Daily Mail ta rahoto cewa ana yunkurin hana amfani da dogon Hijabi da ake kira burqah a Kasar Jamus. Shugaban Kasar Jamus, Angela Me...
Rating :
5