Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun mamaye Babban kotun tarayya da ke Abuja inda suka gudanar da zanga zangar nuna kin jinin kungiyar Shi'a tare da nuna rashin Jin dadi kan hukuncin kotun wadda ta nemi a saki Shugaban Kungiyar, Malam Ibrahim El Zakzaky.
Masu zanga zangar wadanda ke dauke da kwalaye da ke dauke da sakonni na neman tsige Alkalin da ya zartar da hukuncin Sakin El Zakzaky. Masu tarzoman sun nuna cewa Sakin El Zakzaky zai jefa jami'an tsaron kasar nan cikin hadari kuma zai halatta ayyukan ta'addanci a kasa.
Title :
An Gudanar Da Tarzoman Kin Jinin Shi'a A Abuja
Description : Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun mamaye Babban kotun tarayya da ke Abuja inda suka gudanar da zanga zangar nuna kin jinin kungiyar Shi...
Rating :
5