Yan bangar siyasa a Jahar Rivers sun hallaka mataimakin Sufritandan ‘yan Sanda Alkali Mohammed yayin da ake gudanar da zaben da aka yi a ranar Asabar.
‘Yan bangar sun yi wa Babban jami’in kwantar bauna ne a garin Omoku da ke karamar hukumar Onelga a jahar, inda suka sare kan sa, da na mai tsaron sa.
An samu rahotanni da dama na rikici da kashe kashe,
da satar akwatinan zabe yayin da ake gudanar da zaben ‘yan majalisun da za su wakilci jahar a majalisun jahar da na tarayya.
Jahar Rivers dai dama ta yi kaurin suna a tashin hankali lokacin zabe, kamar yadda aka gani a zaben shekarar 2015 da kuma zaben cike gurbin da ya kasa kammaluwa saboda hare-haren da suka kai ga kisan jami’in zabe da masu kada kuri’a.
Title :
An Gillewa Wani Jami’in Dan Sanda Kai a Lokacin Zaben Jahar Rivers
Description : Yan bangar siyasa a Jahar Rivers sun hallaka mataimakin Sufritandan ‘yan Sanda Alkali Mohammed yayin da ake gudanar da zaben da aka yi a ran...
Rating :
5