Daga Ubaidullah Yahaya Kaura
Tabbas abun akwai mamaki a ce ana tura yara mata karatun almajiranci kuma musamman a ce a jihar Zamfara kuma ma wai a babban birinin jiha.
Makarantar dai an gano tabne a unguwar Janyau dake yammacin garin Gusau inda ake kiran makarantar da sunan Makarantar Malam Ibrahim wanda akasarin Alamajiran makarantar mata ne masu kananan shekaru wanda ya kamata a ce suna kusa da iyayensu domin kula da tarbiyarsu da duk sha'anin rayuwarsu.
Wani abun takaici shine wadannan yara Mata sune ke zuwa bara, ko aikatau domin su nemowa kansu abunda za su saka abakinsu kamar dai yadda yara maza almajirai ke tangangara suna bara abincin da za su ci.
Da ake zantawa da wata yarinya almajira dake Makarantar a wani shiri da gidan Radio na jihar Zamfara ya wallafo Yarinyar cikin sheshekar kuka ta bayyana cewa sai sun yi aiki mai matukar wahala a gidajen al'ummma kafin su samu abinci, haka kuma ta bayyana suna da yawa domin adadinsu ya kai 100 kuma suna kwana a daki guda cikin matsuwa ga rashin tsafta.
Sudai wadannan yara mata akasarinsu uwayensu na daukosune daga kauyuka batare dason ransuba.
Tabbas wannan abu cin zarafin yara ne, taka hakkin bil'adama ne, yau ko yara maza da ake turawa Alamajiran ci ya suka Kare, suna karewane alalace, awahalce Wani lokacima sune ke zama fitina ga alummmah. Tau ballantana yara mata da kodayaushe yakamata suna tare da iyayensu, wanda ko ahakanma ya aka Kare ballanta ace ansakesu ga banza awannan lokaci rayuwa ta gurbace.
Malammai dayawa sun bayyana rashin ingancin ita kanta bara da ake tura yara maza ballantana mata, wanda baida asali ga addini. Tabbas neman ilimi wajibine ga kowa amma kuma akwai yadda musulunci ya tsara.
Wajibi ne uwaye su tarbiyantar da yaransu bawai su sake su tamkar shara ba suna tangarara domin Allah zai hukuntasu akan tarbiyar yaransu.
Haka kuma gwamnati ta kara kaimi ta yi bincike wajen tabbatar da kawar da wannan mummunan abu kai idanma sonsamune ko yara maza a hana su yawon bara ballantana yara mata.
Title :
An Gano Makarantar Da Ake Alamajirantar Da Yara Mata A Garin Gusau
Description : Daga Ubaidullah Yahaya Kaura Tabbas abun akwai mamaki a ce ana tura yara mata karatun almajiranci kuma musamman a ce a jihar Zamfara kuma ...
Rating :
5