Shahararren Mai bada umarnin kuma Producer a Kannywood Kamal S Alkali ya bayyana a shafin sa na Instagram cewa idan har ba’a daina gareje a masana’antar wajen samar da Labarai ba za’a samu karancin Fina Finai masu Inganci.
ya ce “Dole mu rika kula da hakkin masu sayen fina finan mu ta hanyar inganta labarai sabbi, nazari ne kadai zai kara bun kasa masana’antar da kuma daidai kunmu. shi labari mai kyau amfanin shi bashida adadi ko iyaka, kuma babu wanda ysan lokacin da ka tafi gun masana neman shawara suna nan kuma ba kudi ake basu ba kai ne mai riba idan kayi garaje jarin da aka zuba zai lalace waye da asara?”
Wannan bayanin Nasa yaja hankullan mutane da inda sukayi ta bayyana ra’ayoyin su akan wannan bayani nasa. daga ciki akwai shahararren mai bada umarnin nan Hassan Giggs inda ya bayyana cewa “Harkan Fim ta canza sossai daga yadda muka santa domin kuwa yanzu Labarin FIm shine babban abun dubi. dan Haka ya Mai hada fina finai ya kamata suyi kokarin sossai domin ganin anyi abunda ya dace”.
Ko menene naka ra’ayin
Daga mujallarmu.com
Title :
Akwai Yiwuwar Kakarancin Fina Finai Masu Inganci Nan Gaba– Kamal S Alkali
Description : Shahararren Mai bada umarnin kuma Producer a Kannywood Kamal S Alkali ya bayyana a shafin sa na Instagram cewa idan har ba’a daina gareje a ...
Rating :
5