A karshe,Masana kimiyyar magunguna sun samun nasara samu wata allurar rigakafi da ake sa ran za ta yi tasirin kashe kwayar cutar Ebola wadda ta yi sanadiyyar salwantar daruruwan rayuka.
An dai yin gwajin allurar ne a daya daga cikin kasashen yammacin Afurka da cutar Ebola ta yi wa mummunar illa, wato kasar Guinea kasar da sai a shekarar nan aka kakkabe cutar daga ciki.
Sakamako na karshe da aka wallafa a mujallar Lancet ta Birtaniya, ya nuna dukkan mutane kusan sittin da aka yi musu allurar, bayan kwana 10 da aka sake gwada su sai aka ga babu wannan cutar a jikinsu.
Ya yin da wasu sittin da ba a yi musu riga-kafin ba, kusan ashirin da uku sun kamu da cutar. Daraktan cibiyar bincike a Birtaniya the Wellcome Trust, ya ce samar da riga-kafin cutar Ebola abu ne da ya kamata a yaba da shi. Fiye da mutane dubu goma sha daya ne suka mutu a kasashen da cutar Ebola ta fi kamari a yammacin Afurka, wato Guinea, da Laberia da kuma Saliyo.
Title :
A Karshe An Samu Maganin Rigakafin Cutar Ebola
Description : A karshe,Masana kimiyyar magunguna sun samun nasara samu wata allurar rigakafi da ake sa ran za ta yi tasirin kashe kwayar cutar Ebola wadd...
Rating :
5