Daga Rariya
A yau Labara ne za a gwada wani sabon maganin cutar HIV a kasar Afirka ta Kudu wacce ke cikin kasashe na gaba-gaba wajen masu fama da cutar a duniya.
Masana kimiyya sun ce gwajin shi ne mafi girma da zurfi da za a yi a kasar.
Kimamin mutum miliyan bakwai ne a Afirka ta Kudu ke dauke da cutar, yayin da mutum dubu daya ke kamuwa da ita a kullum.
Masana daga Amurka, wacce ke daukar nauyin gwajin, sun ce suna fatan gwajin shi ne na karshe da zai zama silar gano maganin cutar kwata-kwata.
Za a yi gwajin ne bayan an yi irin sa a kasar Thailand a shekarar 2009, wacce a yanzu take da kashi 30 na garkuwa ta kamuwa da cutar.
Ana sa ran za a fitar da sakamakon gwajin nan da shekara hudu masu zuwa.
Title :
Za A Yi Gwajin Sabon Maganin Kanjamau A Afirka Ta Kudu
Description : Daga Rariya A yau Labara ne za a gwada wani sabon maganin cutar HIV a kasar Afirka ta Kudu wacce ke cikin kasashe na gaba-gaba wajen masu ...
Rating :
5