Gwamnatin Najeriya ta bayyana fargabar cewa irin yadda ake fitar da kayan abincin da aka noma a bana daga kasar ka iya jefa al'ummarta cikin matsalar karancin abinci a badi.
Gwamnatin dai ta yi kiyasin cewa akalla ana fitar da hatsi cike da manyan motocin daukar kaya kimanin 500 a kowane mako zuwa wasu kasashen Afrika.
Sai dai Babban Mai Ba Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce a yanzu gwamnatin ta fara daukar matakan shawo kan matsalar.
''Shugaban kasa ya saki kudade masu yawa ga ma'aikatar gona. Yanzu ma'aikatar ta fara saye wadannan kayan abincin ana ta laftawa a rumbuna don a ajiye.'' In ji mai magana da yawun shugaban kasar
Source Rariya
Title :
Za A Iya Fuskantar Karancin Abinci Sakamakon Fita Da Hatsi Waje - Garba Shehu
Description : Gwamnatin Najeriya ta bayyana fargabar cewa irin yadda ake fitar da kayan abincin da aka noma a bana daga kasar ka iya jefa al'ummarta c...
Rating :
5