Shugaban hafsan sojojin Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa kashi 60 cikin dari na 'yan Boko Haram ba 'yan
Nijeriya bane.
Janar Buratai ya bayyana hakan a jiya
Laraba, yayin da yake tarban wakilin sakataren majalisar dinkin duniya na
musamman Dr. Mohammed Ibn Chambas a
hedkwatar Operation Lafiya Dole a Maimalari Cantonment dake jihar Borno.
Ya kuma bayyana cewa 'yan ta’addan suna kan shan kashi a hannun sojoji, kuma rundunar sojoji za su ci gaba da yin artabu
har sai 'yan ta’addan sun mika wuya daga karshe.
A nasa jawabin Ibn Chambas ya yi amfani da taron gurin yin ta’azziya ga gwamnatin tarayya, sojojin Nijeriya, da kuma iyalan marigayi Kanal Muhammad Abu-Ali wanda 'yan ta’addan suka kashe tare da sojoji shida a ranar 4 ga watan Nuwamba.
Title :
Yawancin 'Yan Boko Haram Ba 'Yan Nijeriya Ba Ne, Inji Janar Buratai
Description : Shugaban hafsan sojojin Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa kashi 60 cikin dari na 'yan Boko Haram ba 'yan Nijeriy...
Rating :
5