Yansanda sun hallaka wasu yan fashi su biyu a yayin barin wuta da aka yi tasakninsu a jihar Delta.
Jaridar Daily Post ta ruwaito barayin sun je yin fashi ne ga wani mutum a kan titin Warri zuwa Sapele da misalin karfe biyu na dare a ranar talata 1 ga watan Nuwamba. Rahotannin sun bayyana cewa barayin sun yi ma mutumin fashin N300,000, wayoyi guda uku da sauran kayayyaki, inda daga bisani suka arce a cikin keke NAPEP.
Nan da nan wanda aka yi ma fashin ya kira yansanda, wanda su kuma suka bi sawun yan fashin zuwa mahadar titin Agbassa, inda aka fara musayar harbe harbe tsakanin yan fashin da yansandan, hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan fashi biyu tare da jikkata daya da ya gudu.
Kaakakin rundunar yansandan jihar Celestina Kalu ta tabbatar da faruwar lamarin “an kwato harsasai, da karamar bindiga, da Keke NAPEP. Sa’annan an mika gawan su zuwa dakin ajiyar gawawwaki”
A wani labarin kuma, an hangi wasu yansanda su biyu suna baiwa hammata iska. Yansandan dake sanye da kayan sarki sun dambace ne a bainar jama’a, kuma duk kokarin da aka yin a shiga tsakaninsu bai cimma gaci ba.
Title :
Yan Sanda Sun Kashe Yan Fashi Biyu A Musayar Wuta
Description : Yansanda sun hallaka wasu yan fashi su biyu a yayin barin wuta da aka yi tasakninsu a jihar Delta. Jaridar Daily Post ta ruwaito ba...
Rating :
5