'Daga Jaridar Rariya
Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa wasu 'yan fashi da makami sun tare tawagar wasu motoci dauke da amarya da kawayenta, inda suka yi wa wasu daga cikin su fyade bayan sun yi musu fashi.
Tawagar motocin wadanda za su kai guda takwas sun hadu da 'yan fashin ne a daidai garin Ciranci a lokacin da suke tahowa daga garin Kankia zuwa Daura a daren yau.
Wani ganau ba jiyau ba ya tabbatar mana da cewa daga cikin matan da aka yi wa fyaden har da wata yarinya wadda shekarunta ba su wuce sha daya ba.
Wasu daga cikin matan sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan fashin suna sanye ne da kakin sojoji da na 'yan sanda, sannan kuma sun yi ta harba bindagu ne sama a lokacin da suka tare su.
Yanzu haka dai an garzaya da wadanda aka yi wa fyaden zuwa asibiti mafi kusa a garin na Ciranci domin duba lafiyarsu.
Title :
Yan Fashi Sun Yi Wa Tawagar Amarya Fyade A Jihar Katsina
Description : 'Daga Jaridar Rariya Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa wasu 'yan fashi da makami sun tare tawagar wasu motoci dauke da ama...
Rating :
5