Wani fitaccen malamin tarihi a jami’ar Bayero ta jihar Kano (BUK) Farfesa Dahiru Yahaya ya bayyana kansa a matsayin mabiyin Shi’a inda ya ce, lokaci ya yi da za su fito su bayyana ko su waye ba boye-boye.
“Ni dan Shi’a ne, menene shi’a? Shi’a shine mai goyon bayan Manzon Allah da Iyalan gidan sa."
Ya ce, a wannan zamanin da masu auren jinsi suke fitowa kan titi suna bayyana aikin su sai kai da ke addini za ka ki? Don haka ko ina muke mu shi’a ne ba boye-boye kuma Izzah a hannun mu take.
Shaihun malamin jami'ar ya kuma kalubalanci dokar haramta ayyukan kungiyar Shi'a ta Islamic Movement of Nigeria da jihohin Kaduna da Filato suka kafa, inda yake cewa hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Ya ce, ina jin wani wai ya soke Islamic Movement to, Ni shi’a ne ma ga shakiyyin da ya isa ya soke ta, sai dai ka soke kanka, za mu cigaba da fadin, Ya Hussain.
Zuma Times Hausa
Title :
Wani Farfesa Dan Shi'a Ya Kalubalanci Masu Kyamar Shi'a
Description : Wani fitaccen malamin tarihi a jami’ar Bayero ta jihar Kano (BUK) Farfesa Dahiru Yahaya ya bayyana kansa a matsayin mabiyin Shi’a inda ya c...
Rating :
5