Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da jita-jitar cewa shi da wasu shugabannin jam'iyar APC suna takun saka da daya daga cikin kusoshin jam'iyar Asiwaju Bola Tinubu.
Shugaba Buharin ya bayyana cewa irin wannan jita-jita ba ta da tushe ballantana makama.
Babban mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce shugaban kasar ya nuna matukar bacin ransa game da batun.
Ya ce shugaba Buhari ya sha tattaunawa da Bola Tinubu tun kafin lokacin zaben gwamnan jihar Ondo da kuma bayan zaben.
Tun bayan sabanin da aka samu a zaben fitar da gwani na jam'iyyar a jihar Ondo, rashin jituwa take kara fitowa fili a jam'iyyar.
Hakan ne ya sa wasu ke zargin cewa magoya bayan Buhari na kokarin ganin bayan Tinubu, wanda shi ne ya jagoranci kafa jam'iyyar.
Malam Garba Shehun ya kara da cewa duk wani shaci-fadin da ake yi cewa shugaban kasa da 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin ganin bayan Tinubu, ba shi da tushe.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ya dauki Tinubu a matsayin wani gagarabadan dan siyasa, wanda kowa ya san irin gagarumar gudummawar da yake bayar wa wajen cigaban jam'iyya mai mulki.
Malam Garba Shehu ya shawarci masu jita-jita da su daina kokarin ganin kawo cikas tsakanin shugaban kasa da Tinubu ko kuma jam'iyya.
Ya ce shugaba Buhari na alfahari da ''Jagaba'' (Tinubu) da kuma rawar da yake takawa a cikin jam'iyyar.
Source BBC Hausa
Title :
Tinubu Gagarabadan APC Ne - Buhari
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da jita-jitar cewa shi da wasu shugabannin jam'iyar APC suna takun saka da daya daga ciki...
Rating :
5