A jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya ana ta cece kuce kan yunkurin gwamnatin jihar na gina masallatai a fadin jihar.
Su dai 'yan hamayya na zargin gwamnatin da kashe makuden kudade don gina masallatai 90 a jihar.
Bangaren 'yan hamayyar sun kuma bayyana cewa ba ta fannin gina masallatai ya kamata gwamnati ta kashe kudaden ba, akwai wasu fannoni da suka hada da samar da makarantun firamare da kuma inganta albashin malamai a jihar.
To sai dai gwamnatin jihar ta ce ayyukan da aka shirya yi na daga cikin ayyukan da wakilan al'umma suka bukata, kuma abinda za'a kashe wajen gina masallatan bai taka kara ya karya ba.
Mataimakin gwamnan jihar Barister Ibrahim Hassan Hadejia ya shaida wa BBC cewa daga cikin abubuwan da za a gina har da makarantu da cibiyoyin taruwar al'umma.
Title :
Takaddama Kan Gina Masallatai A Jihar Jigawa
Description : A jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya ana ta cece kuce kan yunkurin gwamnatin jihar na gina masallatai a fadin jihar. Su dai ...
Rating :
5