A wani mataki na mayar da martani, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya yi ikirarin cewa son mulki ko ta halin kaka ya sa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ke kin mutunta Shugaban Kasa Muhammad Buhari.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wata hira da aka yi da Atiku Abubukar inda ya zargi El Rufa'i da tsohon Shugaban EFCC, Nuhu Ribaduda yaudararsa inda Gwamnan ya nuna cewa yana daga cikin kwadayin mulki ya sa tsohon Shugaban kasan ya kintsa rikicin majalisar tarayya ta yadda wasu suka bijirewa umarnin uwar jam'iyyar wajen zaben shugabanni.
El Rufa'i ya kara da cewa tuni tsohon Mataimakin Shugaban kasa ya fara yakin neman zaben Shugaban kasa na shekarar 2019 inda musanta zargin da Atiku ya yi masa na cewa ya yi masa tayin hannu jarin kamfanin Transcorp a lokacin yana Shugaban hukumar sayar da hannayen jari ta kasa.
Ya kara da cewa a maimakon Atiku ya rika neman bata sunan wasu ya kamata ya mayar da hankali wajen wanke kansa kan zargin wani rahoto na majalisar dattawan Amurka inda ake tuhumarsa da badakalar Dalar Amurka milyan 40 wanda Akan haka ne yake kauracewa Ziyartar Amurka
Title :
Son Mulki Ko Ta Halin Kaka Ya Sa Atiku Bai Mutunta Buhari - El Rufa'i
Description : A wani mataki na mayar da martani, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya yi ikirarin cewa son mulki ko ta halin kaka ya sa Tsohon Ma...
Rating :
5