Sojojin Nijeriya na Bataliya ta 121 aka girke a garin Pulka a jihar Borno sun kashe mayakan Boko Haram 30 a yayin da suka yi tawagar sojojin kwantar bauna a karamar hukumar Gwoza,
Da yake bayani game da batun, Shugaban riko na karamar hukumar Gwoza wanda ke cikin tawagar, Saeed Salisu Sambo ya ce, mayakan Boko Haram din sun fara fasa nakiya daga nan suka fara harbi amma kuma sojojin suka fatattake su tare da hallaka 30 daga cikin mayakan. Ya ce wasu sojoji sun samu raunuka kuma a halin yanzu ana duba lafiyarsu a asibitin sojoji da ke Maimalari.
Title :
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 30 A Gwoza
Description : Sojojin Nijeriya na Bataliya ta 121 aka girke a garin Pulka a jihar Borno sun kashe mayakan Boko Haram 30 a yayin da suka yi tawagar sojoj...
Rating :
5