Dakarun sojojin Nijeriya dake garin Kangarwa a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda 13 a yayin wata farauta da suka fita, inda wasu daga cikin 'yan Boko Haram din da dama suka tsira da harbin bindiga.
Saidai soja daya ya rasa ransa a yayin artabun, yayin da guda uku suka samu rauni.
Sojojin sun kuma yi nasarar karbe makamai da motacin 'yan bindigan a yayin artabun wanda aka dauki tsawon awanni hudu ana fafatawa.
Title :
Sojoji Sun Kashe 'Yan Boko Haram Guda 13 A Garin Kangarwa Dake Jihar Borno
Description : Dakarun sojojin Nijeriya dake garin Kangarwa a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda 13 a y...
Rating :
5